Babban bankin kasar Sin ya tsaida kudurin rage yawan kudin ruwa da aka bada rancen kudi da ajiyewa
Babban bankin kasar Sin ya sanar a jiya Asabar 27 ga wata da yamma cewa, tun daga ranar 28 ga wata, an rage yawan kudin ruwa da aka bada rancen kudi da ajiyewa don samar da sauki ga kamfanonin kasar wajen tara kudi, kana an dauki matakan rage yawan kason kudin da babban bamkin ke bukata a ajiye a wurinsa ga hukumomin hada-hadar kudi na musamman.
Wani jami'in babban bankin na kasar Sin ya bayyana cewa, makasudin matakan da aka dauka shi ne kara kyautata tsarin manufofin kudi, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata, da kuma rage yawan kudin da aka kashe don tattara kudi. (Zainab)