in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana kokarin tabbatar da samar da wutar lantarki a dukkanin kauyuka
2016-01-07 10:56:23 cri
Hukumar makamashi ta kasar Sin, ta gabatar da shirin gaggauta raya makamashi don kawar da talauci a yankuna masu fama da talauci.

A jiya Laraba ne dai hukumar ta bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2020, za a cimma burin samar da wutar lantarki a dukkan kauyuka, tare da kammala ayyukan samar da wutar lantarki ta hasken rana ga masu fama da talauci kimanin miliyan 2.

A fannin kyautata tsarin samar da wutar lantarki a kauyuka kuwa, shirin ya bayyana cewa, ya kamata a gaggauta kafa tsarin samar da wutar lantarki a garuruwa da kauyuka. Za kuma a samar da wutar lantarki ga dukkan garuruwan yankin Tibet da Qinghai, ko kafa tsarin samar da wutar lantarki ta makamashi na bola-jari a yankin, ta haka za a iya samar da wutar lantarki a dukkan kauyuka da yankunan makiyaya.

A fannin samar da wutar lantarki ta hasken rana ga masu fama da talauci kuwa, shirin ya bayyana cewa, za a gudanar da wannan aiki ga mutane 35,700, wadanda ke garuruwa 451 a larduna 15 mafiya fama da talauci, wadanda suke da kyakkyawan yanayin hasken rana. Ya zuwa 2020, mutane masu fama da talauci miliyan 2 ne ake fatan za su samu karin yawan kudin shigar su da kwatankwacin Yuan dubu 3. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China