in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaminista Li Keqiang ya shirya gaggauta raya sha'anin ciniki ta internet a kauyuka
2015-10-15 10:36:04 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya shugabanci taron majalisar gudanarwar kasar a jiya Talata 14 ga wata a nan birnin Beijing, inda ya shirya gaggauta raya sha'anin ciniki ta internet a kauyuka don amfanawa jama'a.

A gun taron, an tsaida kuduri cewa, ya kamata a kara inganta gudanar da cinikayya ta hanyar amfani da yanar gizo a kauyuka, da kyautata yanayin raya irin cinikayya a kauyuka, da samar da yanayi mai kyau na kashe kudi, da yaki da sayar da kayayyaki masu yabu a kan internet, da kuma kara gabatar da manufofi masu dacewa don raya sha'anin.

Hakazalika kuma, an tsaida kudurin kara zuba jari, da jagoranci kananan hukumomi wajen kyautata manufofi da kara samar da kudin goyon baya da dai sauransu don cimma burin shimfida tsarin yanar gizo a kashi 98% na kauyukan kasar Sin a shekarar 2020. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China