in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron kwamitin tsakiyar JKS kan aikin da ya shafi kauyuka
2013-12-24 21:06:12 cri
Daga ranar 23 zuwa 24 ga wata, an yi taron kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS ) kan aikin da ya shafi kauyuka a nan birnin Beijing, inda aka nuna cewa, dole ne a yi kokarin tabbatar da ingancin abinci da sa kaimi ga samun karin kudin shiga ga manoma, a kokarin samar da wata sabuwar hanyar raya aikin gona mai alamar kasar Sin dake bin fasahohin samarwa na zamani da kuma mai karfin takara kwarai ba tare da gurbata muhalli ba.

A gun taron, babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS, Xi Jinping ya yi bayani kan wasu muhimman batutuwa dangane da sa kaimi ga yin kwaskwarima a kauyuka, tare da bayar da bukatu a fili. A nasa bangare, firaministan Sin Li Keqiang ya yi bayani kan shirin da aka tsara da ya shafi kokarin zamanintar da fasahar aikin gona da ayyukan gwamnati na kula da kauyuka, aikin gona, da kuma manoma.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China