Gwamnatin kasar Burundi ta sanar a ranar Talatar nan cewa, ba za ta halarci tattaunawar sulhu na cikin gidanta da za'a yi a Arusha na kasar Tanzaniya ba, tana gardamar cewar ranar da aka saka bai je da yarjejeniyar ba.
Joseph Bangurambona, babban sakatare a ma'aikatar harkokin waje da hadin gwiwar da kasa da kasa ta Burundi a bayanin da ya yi ya ce, babu wata yarjejeniyar da aka tanadi ranar 6 ga wata a matsayin ranar tattaunawar cikin gidan. Hakan na nufin tawagar gwamnatin kasar Burundin ba za su je Arusha ba. Kuma Fara tattaunawaa ranar 6 ga wata lokaci ne da bai dace ba.
Mr. Bangurambona ya jaddada cewar akwai wassu abubuwan da ya kamata a sake canzawa kafin a amince da za a sake dawowa da tattaunawa.
Ya ce, gwamnatin kasar ba za ta amince da tattauna da mutanen da suka zabi tashin hankali ba. Ya nuna cewar wata karin matsala a yanzu ita ce yadda wata mata ta halarci tattaunawar 28 da watan Disambar bara a Entebbe na kasar Uganda, wadda ta yi ikirarin cewa, ita ce shugabar wata kungiyar da ko rajista ba ta da ita.(Fatimah Jibril)