Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya ba da umurnin nada sabbin ministoci 31, da kuma sakatarori biyu a jiya Litinin, a wani mataki na kafa sabuwar majalisar ministocin kasar.
Hakan dai na nufin rabin hukumomin gwamnatin kasar za su samu sabbin ministocinsu, kuma tsohon jakadan kasar dake kasar Faransa Macalle Camara, zai zama ministan harkokin wajen kasar. Kaza lika an nada sabbin ministocin tsaro, da harkokin jama'a, da tattalin arziki da harkokin kudi da kuma sauran muhimman mukamai.
A ranar 21 ga watan Disambar shekarar 2015 ne, Alpha Conde ya zama shugaban kasar Guinea a hukunce, a kuma lokacin ne ya fara wa'adi na biyu na aiki a matsayin shugaban kasar. Daga bisani, bisa tsarin siyasar kasar, firaminista Fofana da kuma dukkan jami'an gwamnati sun yi murabus, domin bada damar kafa sabuwar majalisar dokokin kasar.
A Talatar nan kuma Alpha Conde, ya nada Mamady Youla a matsayin sabon firaministan kasar, wanda shi ne ya jagoranci aikin kafa majalisar ministocin kasar. (Lami)