Babu wani tashin hankali daga bangaren magoya bayan Alpha Conde kamar yadda aka lura a ranar Lahadi a birnin Conakry na Guinea, bayan sun yi bukukuwan murna a lokacin da aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasa na wucin gadi da hukumar zabe mai zaman kanta (CENI) ta fitar a ranar Asabar da yamma.
Sakamakon zaben da ya nuna nasarar shugaba mai barin gado da kuri'u 2 285 827, kimanin kashi 57,85 cikin 100 na kuri'un da aka jefa masa. (Maman Ada)