Yan takarar zaben shugaban kasa na ranar 11 ga watan Oktoba daga bangaren adawa sun bukaci da a soke zaben shugaban kasa, ganin cewa an samu magudi sosai a yayin zaben, in ji shugaban 'yan adawar Cellou Daleon Diallo a ranar Litinin, a yayin wani taron manema labarai.
A cewar 'dan takarar jam'iyyar adawa ta UFDG, shaidun sun nuna cewa, hukumar zabe mai zaman kanta CENI da aka dorawa nauyin shirya zabe, ta shirya magudin zabe, ta yadda 'dan takara mai barin gado, shugaban kasar Guinea Alpha Conde zai ci nasara. (Maman Ada)