in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Guinea ya kaddamar da aikin madatsar ruwa da kamfanin Sin zai gina
2015-12-23 11:07:02 cri

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya kaddamar a ranar Talata, da ayyukan madatsar ruwan samar da wutar lantarki ta Souapiti mai karfin megawatt 450 da kamfanin kasar Sin CWE zai gina.

An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar tsakanin gwamnatin Guinea, bisa wakilcin ministan makamashi, da kuma kamfanin kasar Sin CTG, bisa wakilcin reshensa na CWE, a ranar 29 ga watan Satumba, a gaban idon shugaba Alpha Conde.

Gina madatsar ruwan ta Souapiti zai bai wa Guinea damar cimma burinta na samun 'yanci na makamashi cikin dogon lokaci, da bunkasa masana'antunta tare da kasancewa wata kasar dake fitar da lantarki a shiyyar.

Bisa kara rubanya karfin madatsar ruwan Kaleta ta farko, a kimanin megawatt 450, madatsar ta Souapiti za ta lakume dalar Amurka biliyan 1,5.

Madatsar ruwan, za a gina ta kan kogin Konkoure, sannan za a kammala cikin wa'adin watanni 58, wato kusan shekara biyar, kana an kiyasta cewa, za ta rike ruwa kusan cuba biliyan 3,9.

Bayan ginawar wannan madatsar ruwa, za mu samu wutar lantarki da kuma zarafin bunkasa tattalin arzikinmu, domin duk wani ci gaba sai da lantarki, in ji shugaba Alpha Conde bayan ya kaddamar da bikin fara aikin.

Haka kuma ya nuna fatansa na kara karfafa dangantaka tsakanin kasarsa da Sin a sauran bangarorin tattalin arzikin da na ababen more rayuwa.

Idan dangantaka na ci gaba da karfafa tsakanin Sin da Guinea, za mu fatan kullum wannan dangantaka ta ci gaba da dorewa tare da sauran kasashe domin saukaka gina wasu madatsun ruwa, in ji shugaba Alpha Conde. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China