A jiya Litinin, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana gamsuwarsa dangane da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa zagayen farko a ranar Asabar da ta gabata ba tare da tashin hankali ba.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun babban sakataren, ya bukaci shugabannin siyasa da masu fada a ji a kasar da su gargadi magoya bayansu da su kai zuciya nesa a yayin da ake jiran bayyana sakamakon zaben, sannan ya bukace su da su guji furta duk wasu kalamai da za su tunzura jama'a don gudun barkewar rikici.
Mista Ban, ya sake yin kira ga masu ruwa da tsaki a kasar da su yi iyakar kokarinsu wajen warware duk wata takaddama da ta taso ta hanyar hukumomin shari'a dake kasar.
Duk da cewar an gudanar da zaben salin alim, amma har yanzu tsugune ba ta kare ba kasancewar dukkannin 'yan takara 7 da suke kalubalantar shugaba mai ci, suna bukatar a gudanar da zagaye na biyu na zaben.
Kasar ta Guinea ta jima tana fuskantar tashin hankali, kasancewar shugaban kasar mai ci Alpha Conde, ya daure shugabancin kasar ne ta hanyar juyin mulkin sojoji.(Ahmad Fagam)