Kungiyar tarayyar kasashen Afrika wato AU, ta yabawa al'ummar kasar Guinea sakamakon yadda suka gudanar da zaben shugaban kasa a ranar Asabar din da ta gabata ba tare da tashin hankali ba, duk cewar an dan samu rigingimu kafin aiwatar da zaben.
A sanarwar da shugabar AU Nkosazana Dlamini Zuma ta bayar a ranar Talatar nan, an bayyana cewar, yadda al'ummar kasar Guinea suka yi fitar dando suka kada kuri'unsu sun nuna wa duniya cewar, sun gane muhimmancin zaman lafiya.
Sama da mutane miliyan 6 ne suka fito domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar wanda 'yan takara 8 suka fafata, kuma ana sa ran samun sakamakon zaben a wannan mako.
Sanarwar ta bukaci al'ummar Guinea da su mutunta jawaban hukumomin zaben kasar, kuma su guji tashin hankali.
Tashin hankalin da ya barke gabannin zaben tsakanin bangarorin kasar, ya haifar da zaman dardar a duk fadin kasar.
AU ta tura tawagar jami'an sa ido kimanin 30 zuwa kasar.(Ahmad Fagam)