in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta amince da shirin raya ci gaban yakunan Larabawa
2015-12-31 10:58:17 cri
Gwamnatin Isra'ila ta amince da wani shiri na tsawon shekaru biyar don raya ci gaban yankunan Larabawa, da nufin cike wagegen gibin dake tsakanin al'ummar Yahudawa da kuma Larabawa a yankunan da Isra'ila ke iko da su.

Ministan samar da daidaito na Isra'ila Gila Gamliel, shi ne ya gabatar da shirin, wanda ya samu amincewar Firaiministan kasar Benjamin Netanyahu, da ministan kudin kasar Moshe Kahlon. Wannan shiri ya hada da ware kudade a fannoni dabam dabam ga yankunan Larabawa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, wanda yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 3.9.

Wannan dai shi ne shiri mafi girma da gwamnatin Yahudawa za ta aiwatar, wanda zai daga likafar tattalin arzikin Larabawa 'yan asalin Isra'ila da 'yan Palastinu dake zaune a Isra'ila a matsayin 'yan kasa tun bayan karshen yakin duniya a 1948, wadanda adadinsu ya kai kimanin kashi 20 cikin 100 na yawan al'ummar Isra'ila. Sai dai an dan samu jinkiri wajen amincewa da shirin, sakamakon bijirewar da wasu ministoci daga jam'iyyar Likud ta Mista Netanyahu suka yi. Amma daga bisani an amince da shiri a Larabar da ta gabata.

Kudaden za su shafi inganta samar da kayayyakin more rayuwa, a fannonin sufuri, gidaje, masana'antu, ilmi, kiwon kafiya da kuma walwalar al'ummar Larabawa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China