A ranar Lahadin karshen mako ne aka harba wasu rokoki daga wajen birnin Tyre na Lebanon zuwa Isra'ila, lamarin da ya sanya Isra'ilan maida martani kan garuruwan Qolaile da al-Mansouri na Lebanon.
Wata sanarwa da kakakin Mr. Ban ya fitar, ta ce tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya dake Lebanon wato UNIFIL,na gudanar da bincike da hadin gwiwar mahukuntan rundunonin sojojin kasar Lebanonda na Isra'ila domin gano bakin zaran.
Mr. Ban ya kara da cewa UNIFIL na fatan dukkanin sassan da wannan tashin hankali ya shafa zasu kai zuciya nesa, su kuma kaucewa daukar matakan da ka iya rura wutar rikici.
Yarjejeniya mai lamba 1701 da kasashen biyu suka amincewa a shekakar 2006, ta kai ga cimma nasarar dakatar da dauki ba dadi tsakanin Hezbollah da dakarun Israila, bayan shafe kwanaki 33 suna musayar wuta.