Jamhuriyar Afrika ta tsakiya CAR ta gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisun dokoki a jiya Laraba. Al'ummar kasar miliyan 1 da digo 9 ne ake sa ran za su kada kuri'unsu, don zaben sabon shugaban kasa da kuma 'yan majalisu 140.
'Yan takara 30 ne suka shiga zaben nema shugabancin kasar, da suka hada da wakilan jam'iyyar 'yantar da jama'ar jamhuriyar Afrika ta tsakiya, da kuma jami'an gwamnati. Kana 'yan takara 1790 ne suka shiga zaben majalisun dokokin kasar. Wasu jami'an kungiyar AU da kuma sauran kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya za su sa ido kan wannan zabe.
A baya dai ya kamata a shirya gudanar da wannan zabe a shekarar 2014, amma aka jinkirta sakamakon tashe-tashen hankali a kasar. Manazarta na ganin cewa, wannan zabe zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen rikicin yakin basasa da ya barke a shekarun baya a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.(Lami)