Bisa labarin da aka bayar, an ce, wassu jami'an MINUSCA sun ci zarafin wata karamar yarinya mai shekaru 12 a Bangui babban birnin kasar, kana suka kashe wani karamin yaro da mahaifinsa.
Tawagar ta MINUSCA ta ba da sanarwa cewa, za ta gudanar da bincike game da lamarin, don gurfanar da masu laifi gaban kuliya.
A sa'i daya kuma, sanarwar ta ce, ganin yadda jami'an kiyaye zaman lafiya da suka yi aiki birnin Bangui a ranakun 2 da 3 ga wata suka yi yawa, don haka akwai wahala sosai na binciken lamarin, sabo da haka, ba za a sanar da sakamakon da aka samu yanzu ba.
Bisa labarin da aka samu, an ce, asusun kula da harkokin yara ta M.D.D. UNICEF tana ba da aikin jinya, da agaji a fannin doka don taimakawa wannan karamar yarinya.
A cikin 'yan watanni nan, an tuhumi jami'an tawagar MINUSCA da laifin muzgunawa mata sau da yawa,abin da ya tilasata ma shugaban tawagar MINUSCA Babacar Gaye yin murabus a farkon watan da muke ciki.
Babban magatakardar M.D.D. Ban Ki-Moon ya nuna cewa, majalisar ba za ta lamunce ma jami'an da suka keta doka ba, idan har aka tabbatar da laifinsu, za a yi musu hukunci mai tsanani.(Bako)