in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan tawayen Sudan sun yi ikirarin hallaka sojojin gwamnati a kudancin Kordofan
2015-12-07 09:27:29 cri
A ranar Lahadin nan 'yan tawayen SPLM a arewacin Sudan sun yi ikirarin hallaka sojojin gwamnatin Sudan kimanin 9 a yankin kudancin Kordofan mai fama da rikici.

Mai Magana da yawun dakarun na SPLM Arno Taloudy, ya ce mayakan nasu sun yi nasarar yin kofar rago ga sojojin gwamnati, wadan da suka yi yunkurin shiga sansanin su dake yankin Kadankail da nufin fatattakan dakarun 'yan tawayen dake lardin Dalang.

Taloudy, ya ce sun yi nasarar kashe sojojiin gwamnati 9, amma babu koda mutum guda da ya rasa ransa daga bangaren 'yan tawayen.

Sai dai ya bayyana cewar, matakin da sojojin gwamnatin Sudan ke dauka a kudancin Kordofan, tamkar mayar da hannun agogo baya ne, kan shirin yarjejejniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin bangarorin biyu.

Har yanzu bangaren sojojin gwamnatin Sudan basu ce uffan ba dangane da ikirarin da 'yan tawayen suka yi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China