in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RDC-Congo: Tsofuwar kungiyar'yan tawayen M23 na shirin shiga shawarwari a matsayin wata jam'iyyar adawa
2015-12-09 12:15:39 cri

Tsofuwar kungiyar'yan tawayen M23, wadda sojojin Congo suka samu nasara kanta a cikin watan Nuwamban shekarar 2013 da kuma take hijira zuwa kasashen Uganda da Rwanda, ta bayyana cewa a shirye take na shiga taron sasanta'yan kasa da shugaban Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo (RDC), Joseph Kabila ya kira, in ji Jean-Marie Runiga da ya daga cikin manyan shugabannin M23 a ranar Talata.

Mr.Runiga ya furta cewa, kungiyarsa tana nuna goyon baya kan shirya shawarwarin sasanta'yan kasa, kuma tuni ma suka mayar da kungiyar zuwa wata jam'iyyar siyasa kamar yadda sanarwar Nairobi ta tanada dake bukatar M23 ta kasance a matsayin wata jam'iyyar siyasa. Ya kuma kara da cewa, kungiyar ta rigaya ta kafa jam'iyyar neman makomar al'umma ta ASP da kuma mika kundinta zuwa ga ma'aikatar cikin gida.

Mista Runiga ya jaddada cewa, ASP na da mambobinta a Kinshasa dake nazari kan shawarwarin da suke fatan gabatarwa a yayin taron sasanta'yan kasa.

Runiga yana ganin cewa,taron zai shafi batutuwan dake da nasaba da ajandar zabe, rajistan masu zabe, da yadda za a samar da kudaden shirya zabuka, tsaron zabuka da sauran batutuwan dake da nasaba da dawowar'yan gudun hijirar Congo dake kasashe makwabta, da kuma batutuwan dake kan tebur da suka shafi aiwatar sanarwar Nairobi.

A cewarsa, jam'iyyar ASP, jam'iyya ce ta adawa dake waje, amma nan da'yan kwanaki masu zuwa za ta kasance jam'iyyar adawa ta cikin gida tare da bude cibiyarta a birnin Kinshasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China