Congo na neman wata hanyar cike gibin faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya
Gaban faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, kasar Congo na neman wasu hanyoyi da matakan bunkasa aikin yawon bude ido, wani bangaren dake tattare da muhimmanci, da ya kasance daya daga cikin ginshikai na yawaita ayyukan tattalin arziki. Gwamnatin Congo na samun goyon baya bisa wannan shiri nata daga tsarin bunkasuwa na MDD (PNUD) da kuma kungiyar yawon bude ido ta duniya (OMT). Wadannan kungiyoyi na taimaka wa kasar wajen kafa wata dabara da wani shirin jagora na yawon bude ido. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku