Shugaba Joseph Kabila ya yi kira da a rika daukar matasa cikin rundunar sojojin kasar
Shugaban jamhuriyar demokuradiyyar Congo (RDC-Congo), Joseph Kabila ya yi kira a ranar Lahadi, a yankin Arewacin Kivu, da a rika daukar matasan yankunan Beni sosai cikin rundunar sojojin kasar ta yadda za a samu karfin yaki da 'yan tawayen Uganda (ADF) dake gabashin kasar. A cewarsa, dole a cigaba da yi yaki da 'yan tawayen ADF har sai an karya lagonsu na kawo illa ga al'ummomin dake Arewacin Kivu, da ma kasar baki daya. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku