Jam'iyyun adawar kasar Congo sun bayyana niyyarsu ta shiga babban zabe bisa sharadi
Muhimman jam'iyyun adawa a kasar Congo sun bayyana niyyarsu a ranar Litinin a birnin Brazzaville kan cewa, za su halarci zaben shugaban kasar da aka sanar gudanar da shi a farkon watanni uku na shekarar 2016, amma bisa sharuda biyar. Wadanda suka hada da kafa wata hukumar zabe mai zaman kanta ta gaskiya, yin amfani da na'urar tantance masu zabe, samar da katunan zabe na zamani, yin amfani da takardar zabe guda da kuma shirya aikin rijistan masu zabe na gaskiya da aka tantance sahihancinsa tare da taimakon kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransanci da kungiyar kasa da kasa dake kula da tsare-tsaren zabe. (Maman Ada)