Kungiyar 'yan kwadago da kungiyar masu fafutukar neman sauyi da jam'iyyar CHP mai goyon bayan Kurdawa ne suka shirya taron gangami, inda suka yi kakkausar suka game da lamarin fashewar bom da aka samu a kusa da tashar jiragen kasa a birnin Ankara a safiyar ranar Asabar din da ta gabata, gami da zargin gwamnatin da rashin daukar kwararan matakai don tabbatar da tsaro.
A shekaranjiya ne, wasu kungiyoyi da jam'iyyu suka shirya gudanar da zanga-zangar lumana daga tashar jiragen kasa, amma yayin da jama'ar suka taru ne aka samu harin kunar bakin waken har sau 2. Cibiyar bada agajin gaggawa ta fadar firaministan kasar Turkiya ta fidda sanarwa a daren ranar Asabar cewar, fashewar bom din ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 95, tare da jikkatar wasu 246, kana wasu 65 sun samu munanan raunuka.
Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin. Amma, a ranar 11 ga wata da sanyin safiya, bangaren 'yan sandan Turkiyya ya dauki matakai a lardin Konya ili da ke tsakiyar kasar da lardin Adana da ke kudancin kasar, inda aka cafke mutane 15 da ake zargi da alaka da kungiyar IS. A ranar 10 da ranar 11 ga watan nan, bangaren sojin Turkiya ya tura jiragen saman yaki, don jefa bom a sansanin dakarun jam'iyyar PKK ta Kurdawa da ke arewaci da kudu masu gabashin kasar, kuma an kashe dakaru kimanin 49.(Bako)