Da yake tsokaci ga 'yan jaridun, Wang Yi ya ce, ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a watan Oktoba, za ta kasance muhimmiya wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Birtaniya, kuma ziyarar za ta kasance wani sabon zarafi na raya dangantakar kasashen biyu. Wang ya ce, babban makasudin zuwansa kasar Birtaniya a wannan karo shi ne don tattaunawa da mu'amala bisa manyan tsare-tsare, da zayyana harkokin siyasa, da shirya ziyarar da ake sa ran shugaban Xi zai yi a Birtaniya, wadda za ta kafa tarihi daga dukkanin fannoni.
Wang Yi ya ce, a karkashin kokari daga bangarorin biyu, dangantakar su ta haye kalubaloli da dama, kuma yanzu haka an kai ga raya dangantakar yadda ya kamata. Kaza lika, bangarorin biyu za su yi amfani da damar ziyarar ta shugaba Xi a Birtaniya, don raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga duk fannoni, da kara cusa sabbin abubuwa cikin dangantakar. (Bako)