in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iyalin sarauniyar Birtaniya ya samu karuwar 'ya mace
2015-05-03 16:26:04 cri
A safiyar jiya Asabar ne madam Kate Middleton ta samu karuwar diya mace, a asibitin St. Mary's dake birnin London na kasar Birtaniya.

Tuni dai sarauniyar Birtaniya da sauran iyalan gidan sarautar suka nuna murnar su ga jin wannan labari, yayin da 'yan siyasa da sauran jama'ar kasar ke ta bayyana fatan alherinsu ga wannan karuwa da jikan sarauniyar Birtaniya William, da matarsa Kate suka samu.

Wannan jaririya dai na matsayi na hudu, a jerin gadon saurautar Birtaniya. Yayin da kakanta Charles, da mahaifinta William, da kuma wanta George ke sahun gaba, a jerin magadan gidan sarautar kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China