in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon yayi allawadai da harin da aka kaiwa sojojin MDD a arewacin Mali
2015-11-29 13:32:17 cri
Babban sakatare janar na MDD Ban Ki-moon yayi allawadai a ranar Asabar da harin da aka kaiwa sojojin MDD dake arewacin Mali, tare da jaddada wajabcin gaggauta gufanar da wadanda suka kai harin gaban kotu.

Mista Ban ya nuna damuwa sosai da wannan hari kan wani sansanin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali (MINUSMA) dake Kidal, inda sojojin majalisar biyu suka mutu tare da wani farar hula ma'aikacin MDD, in ji wata sanarwa ta bakin kakakinsa.

Wasu mutane dauke da makamai sun harba rokoki kan sansanin MINUSMA dake Kidal tare da kashe sojojin MDD biyu 'yan kasar Guinee tare da wani farar hula ma'aikaci dan kasar Burkina Faso. Haka kuma wasu karin mutane ishirin sun ji rauni, hudu daga cikinsu sun ji munanan raunuka.

MINUSMA ta dauki matakan gaggawa domin taimaka wa wadanda suka jikkata tare kuma da cigaba da karfafa tsaro da kare ma'aikatanta, in ji sanarwar. Tare da jaddada cewa wadannan hare hare kan tawagarta ba zasu hana niyyar MDD ba na tallafawa gwamnati da al'ummar kasar Mali kan kokarinsu na cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali. Mista Ban ya jaddada fatansa na ganin an gurfanar da masu hannu kan wannan dayen aiki gaban kotu cikin gaggawa, tare da nanata cewa hare haren dake shafar sojojin MDD na kasancewa manyan laifukan yaki bisa dokokin kasa da kasa.

A nasa bangare, kwamitin tsaro na MDD yayi allawadai da harin na Kidal da babbar murya, tare da yin kira ga gwamnatin Mali data gaggauta yin bincike domin gurfanar da masu laifin harin gaban kuliya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China