in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 42 sun mutu yayin artabu tsakanin kungiyar IS da dakarun Iraqi a lardin Anbar
2015-08-17 12:58:36 cri

Wata majiya daga hukumar tsaron kasar Iraqi ta ce, kimanin mutane 42 ne suka hallaka a ranar Lahadin nan sakamakon harin kunar bakin wake da kuma fafatawa tsakanin mayakan kungiyar IS da sojojin Iraqi a yammacin lardin Anbar dake kasar ta Iraqi.

Hari na farko ya yi sanadiyyar hallaka dakarun Iraqin da mayakan sa kai na Hashd Shaabi dake marawa sojojin Iraqin baya kimanin 15, sannan ya jikkata mutane 8, yayin da dan kunar bakin waken ya ratawa bomb a jikinsa ya nufi inda wata motar sojoji take a kusa da makarantar horas da sojoji a Saqlawiyah da ke arewacin birnin falluja wanda mayakan kungiyar ta IS suka kwace, wanda ke da tazarar kilomita 50 daga birnin Baghadaza, kamar yadda majiyar ta shedawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua wadda kuma ta nemi a sakaye sunanta.

Fadan dai ya kaure ne bayan karin wasu jerin hare hare wadanda suka yi sanadiyyar tarwatsa motocin sojoji kimanin 6, sannan suka lalata wani sashe na ginin makarantar horas da sojojin, amma majiyar ba ta yi karin haske kan irin barnar da aka yiwa mayakan kungiyar ta IS ba.

Sai dai majiyar ta ce an kashe mayakan kungiyar ta IS 4, kuma an raunata 7 daga cikinsu yayin wani harin da dakarun na Iraqi suka kai da tankar yaki a kan sansanin mayakan na IS a Saqlawiyah da Mukhtar kusa da Fallujah.

Haka zalika dakarun na Iraqi tare da tallafin mayakan sa kai na Hashd Shaabi sun yi nasarar hallaka mayakan IS kimanin 20 a kudancin Ramadi wanda ke da tazarar kilomita 110 daga yammacin birnin Baghadaza.

Majiyar dai ta kara da cewar, dakarun na Iraqi tare da tallafin mayakan sa kan sun yi nasarar kwace ikon kauyen Hemeirah dake kudancin Ramadi da wasu sansanonin na kungiyar ta IS dake Mal'ab a kudancin gundumar Ramadi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China