Kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya shaidawa taron manema labarai cewa, jami'in MDD mai kula da harkokin jin kai da 'yan gudun hijira a kasar Afirka ta Tsakiya Aurelien A. Agbenonci, da hukumar kula da harkokin jin kai ta kasar sun nuna damuwa sosai game da matakin da hukumar shirin mika mulkin kasar Afirka ta Tsakiya ta dauka na hana 'yan gudun hijirar kasar kada kuri'u a zaben shugaban kasar da za a gudana, da kuma irin mummunan tasirin da hakan zai yi ga kokarin da ake na yin sulhu a kasar
Dujarric ya kara da cewa, jami'in kula da harkokin jin kai na kasar ya ce, wannan kuduri zai yi tasiri ga ingancin zaben da za a yi a kasar.
Tun a watan Disamba na shekarar 2013, kashi 25 cikin dari na jama'ar kasar Afirka ta Tsakiya ne suke warwatse a cikin kasar, kuma fiye da dubu 460 sun tsire zuwa kasashen Kamaru, Congo, Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo (DRC) da kuma Chadi.
Dujarric ya ce, wannan adadi yana da yawan da zai yi matukar wahala a kau da kai a kansa. (Zainab)