in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar MDD ta yi kira da a dauki matakan gaggawa kan jamhuriyar Afirka ta tsakiya
2014-03-21 10:25:39 cri
Babbar jami'ar MDD mai lura da ayyukan jin kai Navi Pillay ta yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukar matakan tallafawa fararen hula a jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ne ya rawaito Pillay na bayyana wa manema labaru hakan a Bangui, babban birnin Afirka ta tsakiya.

Ya ce Pillay ta bayyana matukar damuwa kan yadda kawo yanzu ake ci gaba da yi wa fararen hula kisan gilla, musamman a wasu gundumomi biyu na birnin Bangui, duk kuwa da tsagaita wutar da ake ganin an yi a wasu yankunan kasar.

Ta ce gaba da kin jinin juna tsakanin sassan da ba sa ga maciji da juna ta ta'azzara a wannan kasa a daidai lokacin da kuma ake kamfar tallafin kudaden gudanar da ayyukan jin kai daga kasashen duniya.

Daga nan sai ta bayyana matukar bukatar da ake da ita, ta hanzarta mai do da doka da oda, tare da tabbatar da kare hakkokin bil'adama a kasar.

Fadace-fadacen dake aukuwa a wannan kasa dai sun hallaka dubban fararen hula, tare da sanya kusan rabin al'ummar ta fada wa mawuyacin halin bukatar agajin jin kai.

Bugu da kari akwai kimanin mutane 650,000 da suka gujewa matsugunnansu a cikin kasar, da karin wasu mutanen sama da 290,000 wadanda suka tsallaka zuwa makwaftan kasashen, baya ga musulmi kusa 15,000 dake zaman zulumi karkashin kariyar tawar ba da agaji ta kasa da kasa a sassan birnin Bangui daban daban. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China