Mr. Ban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ya ce zartas da wannan kuduri muhimmin mataki ne, da zai kawo karshen tashe-tashen hankula dake aukuwa tsakanin dakarun sa kai na musulmi da na mabiya addinin kirista, rikicin dake neman kaiwa ga kisan kiyashi a kasar.
Sanarwar ta kuma ruwaito Ban na yabawa kokarin da rundunonin MISCA, da ta kasashen Turai dake aikin kare zaman lafiya a Afirka ta tsakiyar, yana mai cewa MDD za ta ci gaba da hada kai da su wajen karfafa ayyukan sabuwar rundunar MINUSCA.
Karkashin wannan kuduri na kafuwar rundunar MINUSCA dai kwamitin na tsaro zai samar da dakarun tsaro 10,000, wadanda suka hada da masu sanya ido 240, da masu aikin soji 200, da kuma 'yan sanda 1,800.
Har wa yau, kwamitin tsaron ya yanke shawarar mika ikon rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasashen Afirka MISCA zuwa ga sabuwar rundunar ta MINUSCA a ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa. (Saminu)