Kalaman na Mr. Ban dai na zuwa ne bayan da wasu mahara suka yiwa tawagar jami'an ta MINUSCA kwantan bauna a birnin Bangui fadar mulkin Afirka ta tsakiya a jiya Lahadi, lamarin da ya sabbaba rasuwar daya daga cikin jami'an, kana 8 suka samu raunuka.
Cikin wata sanarwa da kakakin sa ya fitar, Mr. Ban ya yi kira da a gaggauta cafke, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta'asa gaban kuliya. Kaza lika ya yi kira ga daukacin kungiyoyin masu dauke da makamai da su kaucewa kaiwa jami'an wanzar da zaman lafiya hare-hare.
Har wa yau ya jaddada kudurin MDD na ci gaba da goyon bayan mahukuntan kasar, wajen dakile yaduwar laifuka a daukacin yankunan da jami'an wanzar da zaman lafiyar kasar ke gudanar da ayyukan su.
Rahotanni sun nuna cewa tawagar jami'an MINUSCA na kokarin cafke wani mai laifi ne bisa umarnin kotu a birnin na Bangui, lokacin da aka kai musu farmakin.(Saminu Alhassan)