in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayyana sunan sabon jagoran ofishin MDD a Afirka ta tsakiya
2014-05-01 16:42:21 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya bayyana sunan Abdoulaye Bathily daga kasar Senegal, a matsayin sabon wakilin sa a janhuriyar Afirka ta tsakiya.

Sakamakon nadin na sa, sabon wakilin zai kasance jagoran ofishin yanki na MDD ko UNOCA a takaice, wanda ke da hedkwata a birnin Libreville na kasar Gabon.

A cewar mai magana da yawun MDDr Stephen Dujarric, kafin nadin sa, Bathily ya kasance mukaddashin wakili na musamman na magatakardar MDDr, dake aiki da tawagar wanzar da zaman lafiyar kasar Mali ta MINUSMA.

Yanzu haka dai Bathily zai maye gurbin Abou Moussa daga kasar Chadi, mutumin da Mr. Ban ya yi matukar yabawa irin gudummawar da ya bayar, ga ofishin na UNOCA a tsahon wa'adin aikin sa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China