in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun mutu a sakamakon wani harin a birnin Kudus
2015-12-24 11:23:34 cri

Jami'an 'yan sandan Isra'ila sun bayyana cewa, wasu Palesdinawa biyu sun kai hari mutanen Isra'ila ta hanyar yin amfani da wuka a jiya Laraba a birnin Kudus, inda suka hallaka 'yan Isra'ilan biyu, sannan mutum guda ya samu raunuka. An kashe mutum guda daga cikin maharan, sannan wani mutum na daban shi ma ya samu raunuka.

'Yan sanda sun tabbatar da cewa, an kai harin ne a jiya da yammaci wannan rana a kofar Yafo dake tsohon birnin Kudus. 'Yan sanda sun harbi wadanda suka kai harin, kuma guda daga cikin maharan ya mutu, yayin da dayan ya samu raunuka a yayin musayar wuta. Bayan an garzaya da mutane 3 'yan Isra'ila asibiti, biyu daga cikinsu sun mutu a daren jiya.

Ban da haka kuma, hukumar tsaron Isra'ila ta sanar a jiya Laraba cewa, jami'an tsaron Isra'ila sun kama membobin kungiyar HAMAS 25 a birnin Abu Dis na Palesdinu, hukumar ta ce, ta gano wadannan mutane suna shirya kai hare-haren ta'addanci na kisan kiyashi a Isra'ilan.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China