in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Nijar ya zanta da jami'an kafofin watsa labaru na kasar
2015-12-25 10:48:01 cri

A jiya Alhamis ne jakadan kasar Sin dake kasar Nijar Shi Hu, ya zanta tare da shugaban hukumar watsa labaru, kuma shugaban jaridar gwamnatin kasar Adamu, da shugaban kamfanin dillancin labaru na kasar ta Nijar Sadiq da kuma sauran jami'an kafofin watsa labarum kasar.

A gun taron, jakadan na Sin ya bayyana cewa, daga ranar 4 zuwa 5 ga wata, an gudanar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a Afrika ta kudu. Ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da jerin sabbin manufofin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, kana ya gabatar da shirin hadin gwiwa a tsakaninsu nan da shekaru 3 masu zuwa.

Kafofin watsa labaru na kasar Nijar sun watsa labaru a game da wannan taro a dukkan fannoni, matakin da ya samu yabo matuka daga sassa daban daban na al'ummar kasar. Ban da haka kuma, ya yi maraba da kafofin watsa labarun kasar Nijer game da ci gaba da kara wayar da kan jama'a, ta yadda za su kara fahimtar kasar Sin, da ba da gundummawa ga bunkasuwar huldar kasashen biyu.

A nasa bangare, Mr. Adamu ya bayyana cewa, shirin hadin gwiwa a manyan fannoni 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar, zai kara wa kasashen Afrika karfin raya kasa, kuma samar da kudaden tallafi da Sin ke baiwa kasashen Afirka, wanda hakan ke ba su kwarin gwiwa matuka.

A cewar sa a shekarun baya-bayan nan, kasashen Nijer da Sin sun samu sakamako mai kyau wajen gudanar da hadin gwiwa. Kaza lika kafofin watsa labaru na kasar Nijer na fatan ci gaba da yin hadin gwiwa tare da ofishin jakadancin Sin, wajen kara wa jama'ar kasar imani don gane da hadin gwiwar sassan biyu.

A nasa bangare Malam Sadiq, ya bayyana cewa, kamfanin dillancin labaru na kasar Nijer zai ci gaba, da dora muhimmanci kan sakamakon da kasashen biyu suka samu a fannin hadin gwiwa, domin kara wa jama'ar kasar fahimtar moriyar da ake samu, a sakamakon hadin gwiwar Sin da nahiyar Afrika.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China