Bukukuwa nune nunen kayan jiki na FIMA, karo na goma da aka tsaida shiryawa daga ranar 25 zuwa 30 ga watan Nuwamba a birnin Niamey, an dage su zuwa wani lokaci na daban, in ji Seidnaly Sidi Ahmed, da aka fi sani da Alphadi a ranar Litinin a birnin Niamey.
Wannan biki karo na goma da ya kamata a fara yau, an dage shi, domin ni, Alphadi, ina nuna damuwa da abubuwan dake faruwa a duniya, musammun ma a kasar Mali. Dole na amince da matakin da gwamnati ta dauka na gusa wannan bikin zuwa wani lokaci na daban, in ji Alphadi a yayin wani taron manema labarai.
A cewar shugaban FIMA, abin da faru a Diffan Nijar, Mali, Chadi, Kamaru, Faransa, Belgium, na tilasta mana nuna goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya baki daya a shiyyar Afrika, da ma duniya baki daya. (Maman Ada)