in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban diplomasiyyar Aljeriya zai isa Nijar domin yaukaka dangantaka tsakanin kasashen biyu
2015-07-27 10:24:37 cri

Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya, Ramtane Lamamra, zai kai wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu tun daga yau Litinin a Niamey, babban birnin kasar Nijar, domin tattauna batun dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tare da takwararsa ta Nijar madam Kane Aichatou Boulama, da yadda za a kara yaukaka huldar dangantaka da ke tsakanin Nijar da Aljeriya a fannoni daban daban, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya a cikin wata sanarwa.

Wannan ziyara dai na cikin tsarin kara habaka ci gaban huldar abokantaka, makwabtaka da dangantaka dake tsakanin Aljeriya da Nijar, a cewar wannan sanarwa, haka ma wata dama ce ta tabo wasu batutuwan shiyya shiyya da na kasa da kasa da ke da muhimmanci ga kasashen biyu, tare da yin musanya kan muhimman matsalolin da ke kawo cikas ga kwanciyar hankali da tsaro a yankin Sahel da nahiyar Afrika, da kuma tabo wasu batutuwan duniya na ci gaba da kare muhalli.

A cewar wannan sanarwa, wannan ziyara ta zo daidai da jajibirin taron kwamitin hadin gwiwa na kan iyaka na Aljeriya da Nijar karo na 5 da za a bude daga ranar 30 zuwa 31 ga watan Yuli a Niamey a karkashin jagorancin ministocin cikin gidan kasashen biyu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China