Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa, kimanin mutane 40 ne suka hallaka sakamakon wasu hare-hare da mayakan Boko Haram suka kaddamar a yankunan Lamana da Ingoumaoua da ke gabashin kasar.
Gidan rediyon Anfani ya ba da rahoton cewa, mayakan sun harbe wasu daga cikin mutanen ne, yayin da aka tara wasu a cikin wasu gidaje, daga bisani suka banka musu wuta. An kuma garzaya da mutane da dama da suka jikkata zuwa asibitin Diffa.
Har yanzu dakarun kasashen Nijar da Chadi na ci gaba da farautar mayakan na Boko Haram.
Tun a cikin watanni uku da suka gabata ne kasar Nijar kamar sauran kasashen da ke makwabtaka da tafkin Chadi take fuskantar munanan hare-hare daga mayakan na Boko Haram, hare-haren da suka yi sanadiyar rayukan fararen hula da kuma sojoji da dama. (Ibrahim)