in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban Najeriya ya isa Nijar
2015-06-04 10:19:53 cri

Sabon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ya yi rantsuwar kama aiki a ranar Jumma'ar da ta gabata, ya kaddamar da wani rangadin aiki da karfafa dangantakar abokantaka na kwanaki biyu a kasar Nijar, wanda kuma ya kasance rangadinsa na farko a wata kasar waje.

A karkashin wata muhimmiyar tawaga, mista Buhari ya samu tarbo daga takwaransa na kasar Nijar Mahamadou Issoufou a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Hamani Diori da ke birnin Niamey, kewaye da manyan jami'an fararen hula da na sojojin kasar, wakilan jakadun kasashen waje da ke Nijar, da kuma babbar tawagar 'yan Najeriya dake zaune a birnin Yamai.

Rundunar sojojin Nijar ta shiga Najeriya, a cikin wani kawancen, tare da sauran rundunoni, musammun ma na kasashen Chadi, Kamaru da Najeriya, domin yaki da kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China