in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta gaskata labarin mutuwar jagoran Taliban
2015-07-30 09:51:31 cri

A jiya ne fadar shugaban kasar Afghanistan ta sanar da mutuwar jagoran kungiyar Taliban Mullah Muhammed Omar.

Wata sanawar da kakakin shugaban kasar ta Afghanistan Ashraf Ghani ya fitar a jiya Laraba ta ce, ta samu bayanai masu inganci da ke tabbatar da cewa, Mullah Muhammed Omar din ya rasu ne shekaru biyu da suka gabata a kasar Pakistan. Bugu da kari kakakin hukumar leken asirin kasar ta Afghanistan Haseeb Sediqi ya tabbatar da cewa, Mullah Omar ya rasu ne a watan Afrilun shekarar 2013 a wani asibitin da ke Karachi na kasar Pakistan.

Kakakin gwamnatin Afghanistan ya ce, wannan wata dama ce ga dukkan kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar na shiga shirin samar da zaman lafiya a kasar.

Mataimakin kakakin fadar Amurka ta White House Eric Schultz ya ce, koda ya ke bai tabbatar da labarin mutuwar tasa ba, amma gwamnatin Amurkan ta yarda da sahihancin wannan rahoto.

Jama'a daga ciki da wajen kasar suna ta tofa albarkacinsu game da labarin mutuwar jagoran na Taliban, yayin da wakilan kungiyar Taliban din ke tattaunawa ga gwamnatin Afghanistan a kokarin da ake na wanzar da zaman lafiya a kasar.

A 'yan kwanaki masu zuwa ne ake sa ran gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar bayan da sassan biyu suka kammala zagayen farko na shawarwarin makonni da suka gabata a kasar Pakistan.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China