in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin kunar bakin wake a majalissar dokokin Afghan ya sabbaba kisan mahaka 6
2015-06-22 17:45:53 cri

Shugaban rundunar 'yan sandan birnin Kabul a Afghan Abdul Rahman Rahimi, ya ce dauki ba dadin da ya auku tsakanin jami'an tsaro da wasu mahara a majalissar dokokin kasar, ya sabbaba kisan mahara 6 tare da raunata wasu mutane da dama.

Rahimi ya ce a ranar Litinin din nan ne wasu mahara suka kutsa kai cikin ginin majalissar dokokin kasar, suka kuma bude wuta kan al'ummar dake ciki. Gabanin hakan daya daga cikin maharan ya tada wani Bam dake cikin motar da yake tukawa a kofar majalissar, wanda hakan ya baiwa sauran maharan 5 damar shiga harabar majalissar.

Jami'in 'yan sandan bai bayyana adadin wadanda suka samu raunuka sakamakon aukuwar wannan harin ba, sai dai ya ce ya zuwa karfe 12:30 na rana, an shawo kan harin kuma jamai'an tsaro na ci gaba da daukar matakan da suka dace.

Tuni dai kungiyar Taliban ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari, tana mai cewa harin ya yi mummunan tasiri, sabanin rahotannin da tsagin gwamnatin kasar ya fitar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China