Bayan da aka sanar da mutuwar shugaban kungiyar Taliban Mullah Omar, sabanin dake tsakanin bangarori daban daban na kungiyar ya kara tsananta. Har ma wani jami'i mai kula da shawarwari tare da gwamnatin Afghanistan ya yi murabus a jiya Talata sakamakon rashin gamsuwarsa game da sabon shugaba Mullah Akhtar Mohammad Mansoor na kungiyar.
Darektan ofishin siyasa na kungiyar Taliban dake kasar Qatar Syed Mohammad Tayab Agha, ya fidda sanarwar yin murabus daga mukamin sa na darekta, inda cikin sanarwar da ya fitar, Tayab Agha ya zargi tsohon mataimakin shugaba, kuma sabon shugaban kungiyar Mullah Akhtar Mohammad Mansoor da boye labarin mutuwar Mullah Omar har shekaru biyu, wanda hakan a cewar sa kuskure ne a fannin tarihi.
A watan Yuni na shekarar 2013, kungiyar Taliban ta kafa ofishin siyasa a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar domin kula da gudanar shawarwari tare da gwamnatin Afghanistan.
Rahotanni sun nuna cewa bayan da Mullah Akhtar Mohammad Mansoor wanda ke da burin shiga shawarwarin ya zama shugaban kungiyar, sabanin dake tsakanin bangarori daban daban na kungiyar ya kara tsananta. Kafin haka, iyalan Omar sun bayar da sanarwar zargi Mansoor da satar gadon shugaban kungiyar. Kana wasu madugai sun zargi Mansoor na nuna sassauci ga gwamnatin Afghanistan, tare da fatan shiga sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.(Lami)