in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da mummunan harin ta'addanci a birnin Kabul na kasar Afghanistan
2015-08-10 10:29:19 cri

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka dangane da jerin gwanon munanan hare-haren ta'addanci a ranar Alhamis din da ta gabata a birnin Kabul na kasar Afghanistan wanda ya yi sanadiyyar hallaka rayukan jama'a, sannan Majalisar Dinkin Duniyar ta bukaci da a binciko wadanda ke da alhakin kai hare haren domin hukunta su.


Wadannan hare hare sun yi sanadiyyar hallaka rayukan a kalla mutane saba'in tare da jikkata darurruwan jama'a kuma daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da kananan yara, a cewar kwamitin Majalisar Dinkin Duniyar. Ya kuma kara da cewa, kungiyar Taliban ta yi ikirarin cewa, ita ce ke da alhakin kai biyu daga cikin jerin hare haren.


Kwamatin Majalisar Dinkin Duniyar ya bayyana juyayinsa da kuma yin ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su.


Haka zalika kwamitin na Majalisar Dinkin Duniyar ya jaddada aniyarsa na yaki da ta'addanci, wanda ke yin barazana ga zaman lafiyar kasashen duniya.


Majalisar Dinkin Duniyar ta bukaci kasashen duniya da su dauki dukkannin matakan dakile ayyukan ta'addanci wadanda suka dace da kundin tsarin majalisar, musamman kan batutuwan da suka shafi dokokin hukumar kare hakkin bil adama, da 'yan gudun hijira da kuma ayyukan jin kai.(Ahmad Inuwa Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China