in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kungiyar Taliban 45 a yankin arewacin kasar Afghanistan sun yi saranda ga gwamnati
2013-11-11 09:35:38 cri
A ranar 10 ga wata, wani babban jami'in kwamitin samar da zaman lafiya na kasar Afghanistan ya bayyana cewa, a wannan rana, dakarun da ke dauke da makamai na kungiyar Taliban da yawansu ya kai 45 a lardin Baghlan da ke yankin arewacin kasar sun yanke shawarar aje makamansu, inda suka yi saranda ga gwamnatin wurin, kuma suna fatan dawowa da zama a cikin sauran jama'a. Ya ce, yayin ake kara samun dakarun da ke dauke da makamai na Taliban suna yin saranda, aikin tabbatar da zaman lafiya a wurin zai samu kyautatuwa.

Bisa kididdigar da gwamnatin Afghanistan ta bayar, an ce, a cikin watanni 12 da suka gabata, akwai 'yan Taliban kimanin 4000 da suka kwance damara, don shiga cikin shirin gwamnati na samar da zaman lafiya, amma, kungiyar Taliban ta musunta wannan bayanai. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China