A wajen taron, kwamitin sulhu ya zartas da kuduri mai lamba 2254 na amincewa da sakamakon da aka samu a gun taron ministocin harkokin waje na kungiyar goyon bayan Syria ta duniya, kasar Sin ita ma ta jefa kuri'ar amincewa.
Bayan zartas da kudurin, Wang Yi a jawabinsa cewa ya yi, wannan kuduri ya tattara ra'ayoyin kasa da kasa, kuma ya bayyana muhimmiyar rawa da kwamitin sulhun MDD ya taka, tare da zuba sabon karfi na daidaita batun Syria ta hanyar siyasa.