A lokacin bikin cika shekaru 20 da kisan gillar da aka yi wa tsohon firaministan Israila Yitzhak Rabin, ranar Talatan nan magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bukaci dukkan bangarori da su yi tsayin daka na ganin an kauce wa duk wani tashin hankali da makamancin hakan.
Mr Ban bayan haka ya mika ta'aziyarsa ga daukacin al'ummar kasar Isra'ila bisa ga wannan rana da suke tunawa da shi na rasa mutum mai son zaman lafiya, kamar yadda sanarwar da kakakin majalissar ta bayyana.
Mr Ban ta tunatar da cewa, marigayi Rabin ya sadaukar da rayuwan shi wajen samar da tsaro a kasar shi, kuma ya mutu bayan da ya yi matukar kokarin ganin ya samar da dama da bukatar samar da yanayin tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
A cikin shekarun tun bayan mutuwar shi, ta'addanci, fadada yankunan Yahudawa da kawo cikas a duk wani yunkurin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu sai ci gaba yake da wargaza makomar zaman lafiya da ake fatan samu.
Don haka magatakardar na MDD ya bukaci dukkan bangarori da su yi tsayin daka na hana duk wani tashin hankali da tsokanar fada kuma su bi ra'ayin marigayi firaminista Rabin na cewa, hanyar zaman lafiya na hakika da karko ita ce ta yin shawarwari da cimma daidaito.
An dai hallaka Yitzhak Rabin ne a ranar 4 ga watan Nuwambar shekara ta 1995, a karshen wani gangami na goyon bayan tattaunawar Oslo a dandalin Sarkin Isra'ila dake birnin Tel Aviv. Wanda ya yi kisan Yigal Amir ya dage kan kin amincewa da shirin zaman lafiyar da Mr Rabin ya kirkiro, musammam ma rattaba hannu a kan yarjejeniyar ta Oslo a wannan rana.(Fatimah)