A ranar Lahadin nan, Isra'ila ta yi fatali da shirin tattaunawa da kungiyar tarayyar Turai wato EU, dangane da batun tattaunawar zaman lafiya da al'ummar Palastinawa, tun bayan da aka samu rashin jituwa kan wasu kayayyaki da ake samarwa a yankunan na Yahudawa.
Firayin ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda a halin yanzu shi ne ministan harkokin wajen kasar na wucin gada, ya ba da umarnin cewar, za a sake tattaunawa kan rawar da kungiyar EU take takawa cikin harkokin diplomasiyya tsakanin Isra'ila da Palastinu.(Ahmad Fagam)