Sanarwar ta ce, sakamakon hadin gwiwar hukumar lekan asiri da wasu mutanen da abun ya shafa, rundunar sojin kasar ta samu nasarar cafke mutanen 2. Bayan gudanar da bincike ne kuma aka gano cewa wadannan mutane sun fito ne daga wata unguwa da ke wajen birnin Bamako. Yanzu haka dai ana ci gaba da binciken wadannan mutane 2.
Wani jami'in bincike da ya nemi a boye sunan sa, ya shaidawa manema labaru cewa, an samu wata wayar salula a wurin da aka kai harin, wadda ta taimaka ainun wajen cafke wadannan mutane.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 20 ga watan nan na Nuwamba ne aka kai harin ta'addanci kan otel din Radisson BLU dake birnin Bamako, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20, tare da harbe mahara 2 a wurin. (Bako)