A jiya ne shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta, firaministan kasar Modibo Keita, da ministoci 18 na kasar, da dukkan ma'aikatan ofishin jakadancin Sin dake Mali, wakilan hukumomin Sin, da wakilan Sinawa dake kasar Mali da yawansu ya kai 400 suka halarci bikin.
A jawabinsa shugaba Keita ya bayyana cewa, wadannan ma'aikata Sin uku da suka mutu sun zo kasar Mali ne don kawo moriya ga al'umomin kasashen Mali da Senegal, inda suke gudanar da aikin shimfida hanyoyin jiragen kasa a tsakanin kasashen biyu.
'Yan ta'adda sun kashe su ne a yayin da suke kokarin sada zumunta a tsakanin Mali da Sin, don haka sun sadaukar da rayukansu a kokarin inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Mali.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ne aka kai harin ta'addanci a otel din Radisson Blu dake birnin Bamako na kasar Mali, harin da ya yi sanadiyar mutuwar manyan jami'an kamfanin CRCC na kasar Sin guda uku wadanda suka zo Mali don tattauna aikin gina hanyoyin jiragen kasa a tsakanin Dakar da Bamako. (Zainab)