Kwamitin sulhu na MDD, ya zartas da wani kuduri a jiya Laraba, wanda ya yi maraba da aniyar bangarori daban daban na kasar Libya, game da kulla yarjejeniyar siyasa a kasar, yana mai kalubalantar sassan da su amince a kafa gwamnatin hadin kan kasa cikin kwanaki 30 masu zuwa bisa sharuddan da aka amince da su cikin yarjejeniya.
Kudurin ya kara da cewa, kwamitin sulhu na MDD ya yi maraba da yarjejeniyar siyasar kasar Libya, wadda aka kulla a kasar Moroco a ranar 17 ga watan Disambar wannan shekara, tare da fatan kafa kwamiti karkashin firaministan kasar.
Ban da haka kuma, kudurin ya jaddada cewa, kasar Libya tana bukatar kafa gwamnatin hadin kai a birnin Tripoli. Har wa yau kudurin ya kalubalanci kasashe membobin MDD da su daina tuntubar hukumomin da yarjejeniyar siyasar ta kasar Libyan ba ta amince da ita ba.
Bugu da kari, kudurin ya nemi kasashe daban daban da su taimakawa sabuwar gwamnatin Libya, wajen tinkarar kalubalen tsaro ciki har da yaki da kungiyar IS, da kungiyar al-Qaeda da kuma sauran kungiyoyi, idan sabuwar gwamnatin kasar ta nuna bukatar hakan.(Lami)