Samantha Power, wakiliyar kasar Amurka wadda take rike da shugabancin kwamitin na wannan watan ta sanar da hakan lokacin da take zantawa da manema labarai bayan wani tattaunawar sirri da kwamitin ta yi game da Libya.
A safiyar wannan rana, wakilin bangaren adawa na GNC masu ra'ayin addinin Islama a kasar Saleh al-Makhzun shi ma ya tabbatar da wa'adin karshen na rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar. Yana mai bayanin cewa tattaunawar da kwamitin sulhun MDD ta kira shi ne ya fi dacewa. Ya ce wannan yarjejeniyar za ta samar da makoma mai amince ga al'ummar kasar ta Libya.
Libya dai ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan da aka samu majalissan dokoki da gwamnatoci guda biyu masu adawa da juna da kowannen su ke ikirarin jan ragamar mulkin kasar bayan halin rashin tsaro da aka shiga tun kifar da gwamnatin marigayi Mu'ammar Ghaddafi. (Fatimah Jibril)