A wannan rana, kwamintin sulhu na M.D.D. ya zartas da shiri mai lamba 2241 da kuri'un amincewa 13, kana da kuri'un kauracewa 2, don kara wa'adin aikin wanzar da zaman lafiya ga tawagar musamman ta M.D.D. zuwa Sudan ta Kudu, inda Sin ta jefa kuri'ar amincewa.
Liu Jieyi ya ce, Sin ta yabawa M.D.D. kan kokarin da ta yi wajen yin taka tsan-tsan game da saka takunkumi ga Sudan ta Kudu.
Liu Jieyi, yayi fatar cewar matakan da kwamitin sulhu na M.D.D. ya dauka zai yi tasiri a yunkurin samar da zaman lafiya da kawo karshen rikicin a Sudan ta kudu.(Bako)