Ana amfani da hutun na lokacin hunturu ne wajen nazarin abubuwan da suka faru a lokutan baya da masu zuwa a nan gaba misali gasar wasanni da za'a yi a shekarar 2016 na European Championship na Faransa, da batun yin ruf da ciki a kudaden hukumar FIFA da ta UEFA, da abin da ya faru a watan jiya a Bundesliga da nuna damuwa kan yadda kulob din Premier League Ingila zai kasance bayan cece kucen da ake kan batun kara kudaden haraji ga masu amfani da akwatunan talabijin, da abin da matakin zai haifar.
Tabbas dan wasan gaba na kasar Poland Robert Lewandowski ya kafa tarihi, bayan da ya samu nasarar zara kwallaye kimanin 5 cikin mintuna 9 kachal a fafatawa da Wolfsburg. Sannan a farkon zango na shekarar 2015 an wayi gari da samun manyan kanun labarai a jaridu dake wallafa batun maye gurbin Pep Guardiola a kulub din Bayern a kakar wasanni ta badi, inda Carlo Ancelotti zai gaje shi. Sai dai batun yin murabus din Guardiola bai zo da mamaki ba kasancewar ya bada sanarwar hakan tun a 'yan watannin baya.
Kungiyar wasan kwallon kafar Jamus tana fatar da a farfado wasu kulob kulob kamar su Borussia Dortmund, wadanda zasu iya kalubalantar Bayern Munich.
A yanzu haka, amsar tambayar shin ko wanene zai yi nasara a gasar ta Championship, za a iya samun hasashe mabambanta dangane da abin da zai faru a nan gaba. Sannan akwai wani babban gibi da ake sa ran Bayern Munich za ta cike tun da a halin yanzu tana da maki 46 kuma har yanzu akwai sauran wasan da za ta buga.